Amurkawa na ci gaba da jiran sakamakon karshe na zaben Shugaban kasar. Yanzu kallo ya koma wasu jihohi fagagen daga, inda sakamakon wuccin gadi ke nuna ana kankankan, kuma su na iya matukar tasiri wajen sanin wanda zai yi nasara tsakanin dan takarar jam’iyyar Demokarat, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden da Shugaba mai ci dan Republican, Donald Trump.
A New York, an bukaci a kirga duk wata kuri’a a yayin da kasar ke ci gaba da jiran labarin wanda ya yi nasara. Mutane a fadin kasar sun zaku, ciki har da na Pennsylvania, daya daga cikin fagagen daga.
Har yanzu ana cigaba da kirga kuri’u a wasu muhimman jahohi kalilan. To amma bayan da aka bayyana Joe Biden a matsayin wanda ya ci Michigan da Wisconsin – jihohi biyu da Shugaba Trump ya ci shekaru hudu da su ka gabata – Biden ya ce yana da kwarin gwiwar cewa zai samu makin kuri’u (Electoral College Votes) akalla 270, da ake bukata don cin zaben.
Joe Biden, dan takarar jam’iyyar Demokarat, ya ce, “Ba na zo nan don in ce mun ci zaben ba ne, na zo ne don in bayyana cewa idan aka kammala kirga kuri’un, mun yi imanin cewa mu za mu yi nasara.”
Georgia, wace bisa al’ada jihar Republican ce, na daya daga cikin fagagen dagar, inda ake ganin irin goyon bayan da Biden ke da shi a birane da kewaye na iya kai shi ga nasara.
Yayin da ake shirin kidaya kuri’u, Shugaba Donald Trump ya tura sakon twitter jiya Laraba cewa, yana mai ayyana nasara a Pennsylvania, Georgia, North Carolina, da Michigan, ikirarin da Twitter ta bayyana da “marar tabbas.”
Kwamitin yakin neman zaben Trump na shirin rugawa kotu don tsai da kirgen kuri’u a Michigan da Pennsylvania, bisa hujjar cewa ba a barin jam’iyyar Republican ta yi cikakken sanya ido kan yadda kirgen ke gudana.
Shugaba Donald Trump ya ce, “Za mu je Kotun Kolin Amurka. Mu na son a daina duk wata kidayar kuri’u. Ba mu son sun samo wasu kuri’u da karfe hudu na asuba su kara kan adadin kuri’un.”
Willaim Howell wani mai ilimin kimiyyar siyasa a jami’ar Chicago, ya ce: “Kowanne daga cikin ‘yan takarar na da damar bukatar a sake kirga kuri’un idan banbancin da ke tsakani bai kai kashi 1 cikin 100 ba. To amma bisa tarihi sake kidaya kuri’u bai cika haifar da alkaluman da su ka banbanta da na farko ba, don haka ba lallai sake kirgen ya haifar da irin sakamakon da yake so ba.”
Daruruwan magoya bayan Trump sun yi zanga zanga a wani wurin kirga kuri’u a garin Phoenix na jihar Arizona da daren ranar Laraba, su na masu zargin cewa ba a bin ka’ida wajen kirga wasu kuri’un. Da alamar daga karshe dai a kotu ne za a tantance sakamakon karshe na Arizona da sauran jahohin.
Patsy Widakuswara ta Muryar Amurka ta hada wannan rahoton.
Facebook Forum