Har yanzu shirin rage mutuwar kananan yara kafin su cika shekaru biyar da haihuwa yana tafiyar hawainiya a Najeriya. Rahoton halin da kananan yara suke ciki a duniya na shekara ta 2010 ya nuna cewa, Najeriya ce kasa ta 12 da aka fi samun mutuwar kananan yara, inda kimanin kananan yara 143 suke mutuwa cikin dubu daya kafin su kai shekaru biyar da haihuwa.
Rahoton da asusun tallafawa kanannan yara (UNICEF) ya buga, ya nuna cewa, minzanin awon tsawon rai na kafin su cika shekaru 5 da haihuwa a Najeriya ya kai 51, idan aka kwatanta da Niger 54 da Ghana da kuma Afrika ta Kudu mai 52.
Bisa ga rahoton, Najeriya ta dan taka rawar gani, idan aka kwatanta ta da wadansu kasashen nahiyar Afrika kamar Togo da Ghana wadanda minzaninsu ya tsaya 24 da 43 daki daki yayinda aka fi samun mace macen kananan yara da shekarunsu basu kai biyar ba a Afrika ta tsakiya.
Rahotan ya nuna cewa, an sami ci gaba ainun a fannin yiwa kananan yara kasa da shekara daya da haihuwa, allurar rigakafin cututuka dake katse masu hanzari kamar tarin fuka da cutar shan inna da kyanda da da sauransu.
Duk da raba gidajen sauro kyauta da gwamnatin tarayya ta fara gudanarwa shekararu uku da suka shige, inda ake bada gidajen sauro guda biyu a kowanne gida, har yanzu kimanin kashi 42% na iyalai ne kadai suka sami gidajen sauron yayinda kasa da kananan yara kashi 29% suke kwana a karkashin gidan sauro.
A fannin cutar HIV/AIDS kuma, rahoton ya nuna cewa adadin kananan yara kasa da shekara biyar da suka zama marayu ya kai 2,500 a shekara ta 2009.