Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba za a iya shawo kan matsalar gubar dalma ba a jihar Zamfara


Ana kokarin shawo kan matsalar gubar dalma a jihar Zamfara
Ana kokarin shawo kan matsalar gubar dalma a jihar Zamfara

Kwararru sun bayyana cewa, ba za a iya shawo kan matsalar gubar dalma ba a jihar Zamfara, sakamakon yanayin rayuwar al’ummar yankin

Kwararru sun bayyana cewa, ba za a iya shawo kan matsalar gubar dalma ba a jihar Zamfara, sakamakon yanayin rayuwar al’ummar yankin da kuma yadda ake gudanar da ayyukan hakar mu’adinai.

Jami’in sa ido kan gubar dalma kuma daya daga cikin likitocin agaji na Doctors Without Borders, Dr. Ivan Gayton ne ya bayyana haka yayin ziyarar da ya kaiwa ministan tama da hakar mu’adinai Arch Mohammed Musa Sada. Bisa ga cewarshi, abinda kadai za a iya yi a jihar Zamfara shine a sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan hakar mu’adinai.

Sai dai Ivan ya bada tabbacin cewa, ko da yake daruruwan kanannan yara sun rasu da dalilin gubar dalmar, a halin yanzu, kasa da kashi 5% ne ke cikin hadarin mutuwa da cutar sabili da matakan da kungiyar Doctors Without Borders ta dauka wadda take kasha dala miliyan goma kowacce shekara a Najeriya, dala miliyan hudu kuma a jihar Zamfara tunda aka fara samun matsalar gubar dalmar.

Dr. Gayton ya bayyana cewa, magani ba zai zama da amfani ba idan ba a dauki matakin shawo kan abinda ke haddasa cutar ba. Ya kuma yi kira ga ministan hakar mu’adinai ya sa ido domin ganin ana kiyaye ka’idojin hakar mu’adinai.

A cikin jawabinshi, ministan hakar mu’adinan ya ce ma’aikatarshi zata hada hannu da ma’aikatar lafiya da ta kula da muhalli da ayyuka wajen ganin an shawo kan matsalar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG