Jiya Litinin kasuwanin hannaye jarri a turai da Amurka suka fadi a yayinda damuwa da ake nunawa akan rikicin kasuwanci yayi kamari a duk fadin duniya.
Kasuwar hanayen jarin Amurka ta fadi da wajen fiye da kashi daya daga cikin dari a yayinda kasuwanin hanaye jarri a turai suka fadi fiye da haka.
Anyi hasara to amma hanayen jarin fasaha su suka fi dandanawa domin sun fadi da fiye da kashi biyu daga cikin dari. Faduwa mafi girma da aka gani tun watan Afrilu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bada sanarwar shirye shiryen kara kudin haraji akan kayayyaki da China ke sayarwa Amurka, yana misali da damuwa akan matakan tsaro.
Nan da makoni biyu Amurka ke shirin fara kara haraji akan kayayyakin da China ke sayar wa Amurka na fiye da dala biliyan talatin. China tayi alkawarin maida martini nan da nan, matakin daya sa kasashen na duniya guda biyu da suka fi kowace kasar bunkasar tattalin arziki fara rikicin kasuwanci.
Facebook Forum