Kasar China ta gargadi Amurka cewa, ba za a aiwatar da duk wata matsayar cinikayya da aka acimma tsakanin kasashen biyu ba, muudar aka kara kudin fito da kuma daukar wadansu matakan da shugaba Donald Trump ya yi barazana a kan China.
China tayi wannan gargadin ne bayan ganawar sakataren harkokin kasuwanci na Amurka Wilbur Ross da mataimakin Firai Ministan kasar China Liu He a Beijing jiya asabar da nufin dinke barakar harkokin cinikayya tsakanin kasashen inda Beijing ta yi alkawarin rage rarar da ake samu a harkokin cinikayyarta.
Ross ya fada a farkon tattaunawar da aka yi a gidan baki na gwamnati dake Diaoyutai, kasashen biyu sun tattauna musamman kan kayyakin Amurka da China zata saya, sai dai an tashi tattaunawar ba tare da wata sanarwar hadin guiwa ba, kuma babu wani daga cikin bangarorin da ya yi wani Karin haske a kan tattaunawar.
Facebook Forum