Jiya Alhamis jahar New York ta shigar da kara tana bukatar a rusa gidauniyar iyalan Shugaba Donald Trump, bisa hujjar cewa Trump ya yi ta gudanar da haramtattun harkoki na tsawon sama da shekaru gwammai saboda amfanar harkokinsa na kasuwanci da siyasa.
Karar, wadda babbar mai shigar da kara ta jahar kuma 'yar jam'iyyar Democrat, Barbara Underwood ta shigar, ta zargi gidauniyar ta Trump da abin da ta kira, "gagarumin saba ma ka'ida ta wajen hadin baki a siyasance da kwamitin yakin neman zaben Trump da kuma saba ka'idar tafiyar da gidauniyar da ba ta neman riba ba ce."
Karar ta yi zargin cewa Trump, wanda hamshakin attajiri ne mai harkar gine-gine ne gabanin ya rikide zuwa dan siyasa na jam'iyyar Republican, ya yi amfani da kudin gidauniyar wajen biyan kudin lauyoyinsa da tallata otal-otal dinsa da kuma kashe cikin kudin kan wasu harkokinsa. Karar ta ambaci Shugaban kasa da 'ya'yansa uku wato da Donald Trump Jr da Eric Trump da kuma Iavanka Trump, wadanda mambobin kwamitin amintattun gidauniyar ne, a matsayin wadanda ake kara.
Facebook Forum