Amurka ta dau matakin da ka iya tsananta takaddamar da ke tsakaninta da sauran kasashen Yammacin duniya a fagen kasuwanci ta wajen saka haraji da kashi 25% kan karafa da kuma kashi 10 kan dalmar da ake shigo da su daga kasashen Turai da Canada da Mexico kuma harajin zai fara aiki daga yau Jumma'a.
Amurka ta kuma tattauna kan batun takaita shigo da karafa da dalamar daga wasu kasashen da su ka hada da Koriya Ta Kudu da Argentina da Australia da Brazil a maimakon saka masu haraji, abin da Sakataren Harkokin Cinakayyar Amurka Wilbur Ross ya gaya ma manema labarai kenan ta waya.
Shugaba Donald Trump ya sha fadin cewa dole ne a dau irin wannan matakan muddun ana so a tabbatar da ayyukan yi da kuma kamfanoni a wasu muhimman masana'antu a Amurka.
Tuni Firaministan Canada Justin Trudeau ya bayyana harajin a zaman "wani abu da sam ba za a lamunta da shi ba" sannan ya sha alwashin mai da martani.
Shi ma Shugaban kasar Faransa ya ce, "Wannan matakin ba kawai ya sabawa doka ba, ya na kuma cike da kura kurai." ya kara da gargadin cewa, "hada kishin kasa da cinakayya na iya haddasa yaki."
Shugaban majalisar gudanarwa ta turai Jean-Claude, yace matakin na Amurka "Ya saka bakin tabo kan harkokin kasuwanci, kuma babu abunda ya saura, in banda tunkarar kungiyar cinikayya ta duniya, da kuma aza haraji kan kayayyaki d a suke fitowa daga Amurka.
Facebook Forum