Wannan wani mataki ne a ci gaba da kokarin da kasashen yankin ke yi na shawo kan wannan matsala.
Matsalar ta daukan tsatsaurar akida na daga cikin batutuwan da ake ganin na kawo rikice-rikice a yankin.
Shi dai wannan taro ya fi maida hankalie kan matasa, lura da yadda su ke mu’amulla da kafofin sada zumunta na zamani da kuma muggan kwayoyi.
Kasashen Sahel sun hada da Najeriya, Nijar, Mali, Senegal, Burkina Faso, Chad da Sudan da kuma Eritrea.
Domin samun karin bayani kan wannan taro, saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma daga Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar: