Madugun ‘yan adawar mai suna Ousainou Darboe da sauran ‘yan jam’iyyar adawa ta U-D-P dai an yanke musu hukuncin daurin shekaru ukku-ukku ne a watan Yulin da ya gabata, bayanda aka kama su cikin wata zanga-zangar siyasa ta lumana, inda suke neman a yi sauye-sauye ga dokokin zabe na Gambia.
Ganin abinda ya faru, yanzu haka wata jam’iyyar adawa ta Gambia ta fito tana kira da a saki daukacin sauran dukkan fursunonin siyasan dake tsare a kasar.
Saihou Mballow, daya daga cikin jagabannin jam’iyyar G-D-C dake da rassa a kasashen waje yayi kira akan kungiyoyin kare hakkin jama’a irinsu Amnesty International da Human Rights Watch da su sa hannun don sako sauran mutanen da aka tsare a bisa dalilan siyasa.