Yana cikin iyayen babban jami’iyar adawa ta NPP da suka kafa jami’iyyar kuma ya dade ana damawa dashi a jami’iyyar; ya kuma yi paputukar ganin an kawo karshen mulkin kama karya na soji da kuma tabbatar da tsarin demokaradiyya a Ghana.
An dai haifi Nana Addo Dankwa Akuffo Addo kuma ya girma ne a Ga Maami wato tsakiyar birnin Accra ta yankin unguwar Nima.
Mahaifinsa Edward Akufo-Addo yana cikin dattawan Ghana shida da suka kafa jami’iyar siyasa ta farko a Ghana tun kafin kasar ta samu yancin kai kuma mahaifin nashi ya zama shugaban kasa da bashi da cikakken iko daga 1969 zuwa 1972
A shekarar 1992 Nana Addo Dankwa Akuffo Addo shine jami’in tattaro yan jami’iyar NPP na farko, daga bisani ya zama manajan yakin neman zaben dan takarar jami’iyar Farfesa Albert Adu Boahen.
An zabi Akuffo-Addo a matsayin dan majalisar dokoki mai wakiltan mazabar Abuakwa South a jihar gabasahin kasar daga shekarar 1996 zuwa shekarar 2008.
Daga shekarar 2001 zuwa 2007 ya rike mukaman babban minister a gwamnatin tsohon shugaba Kufuor, da farko ya zama babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a har tsawon shekaru biyu sa’annan daga baya kuma ya rike mukamin ministan harkokin waje shekaru biyar.
A wata Oktoban shekarar 1998 Nana Akuffo-Addo ya papata da tsohon shugaba Kufuor a zaben fid da dan takara inda Kufuor ya doke shi kuma ya lashe zaben shuagabn kasar a cikin watan Disemban shekarar 2000 kuma aka rantsar da shi 2001.
Akufo-Addo ya yi murabus daga gwamnatin shugaba Kufuor a cikin watan Yuli shekarar 2007 don shiga zaben fid da gwani na ‘yan takaran shugaban kasa a karkashin jami’iyyar NPP dake mulki a Ghana a waccan lokacin a zaben 2008.
Da ya papata da sauran yan takara 16, Akufo-Addo ya lashe kashi 48% cikin dari na kur’un da aka kada, amma sai a zagaye na biyu masu takarar suka tabbatar da shi ya zamawa jami’iyar dan takaran shugaban kasar.
A cikin watan Maris shekarar 2014 Akufo-Addo ya sanar da niyarsa na neman shiga takararsa a karo na uku a zaben wannan shekarar 2016 – zaben da ake yi a yau.
Ga karin bayani.