A cewar kakakin jam'iyyar MODEL Lumana Afirka mai adawa ta Hamma Ahmadu reshen birnin Konni su ma suna nan kan hanya.
To saidai acewar kakakin jam'iyyar Isa Marei 'yan adawan Gambia sun san ciwon kansu saboda sun yi aiki tare da junansu. Amma a Nijar kowa abun da zai ci yake duba ba muradun kasar ba.kamar yadda 'yan adawan Gambia da Najeriya suka yi. Idan za'a ci nasara dole a duba manufar kasa ba ta mutum ba. Kada a dubi anfanin da mutum zai samu a dubi anfanin da kasa zata samu. Shi ya fi.
Yace kullum mutum yace zai yi gaban kansa ba da wani ba to ko nasara nada wuyar samu.
A jamhuriyar Nijar yawan jam'iyyun siyasa dake cikinta na hana tsayarda dan takara guda a kowane matsayin siyasa daga bangarorin 'yan adawa abun dake raba kuri'unsu su watse.. Kowane lokaci suna kasa kai labari.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.