Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabancin Majalisa: Akpabio Da Tajudeen Muke Goyon Baya - APC


Majalisar Dokokin Najeriya (Twitter/National Assembly)
Majalisar Dokokin Najeriya (Twitter/National Assembly)

A daidai lokacin da ake samun kiraye-kiraye daga Kungiyoyi daban-daban kan shugabancin Majalisar Dokokin Najeriya, a ranar Litinin jam’iyyar APC ta sanar da shiyyoyin da shugabannin Majalisar za su fito.

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki ya yi zama na musamman domin duba rahotannin tuntubar juna da tarurrukan da su ka yi da zababben Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin jam’iyyar har da masu ruwa da tsaki kan yadda za’a raba mukaman shugabancin Majalisar Dokokin Kasa karo na 10.

Bayan taron ne Bala Ibrahim mai magana da yawun jam’iyyar APC ya shaida wa Muryar Amurka cewa, mukamin Shugaban Majalisar Dattawa ya tafi shiyyar Kudu Maso Kudu wanda ake sa ran Sanata Godswill Akpabio shi ne zai rike wannan mukamin.

Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio
Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio

Mataimakinsa kuma ana sa ran zai fito daga Arewa maso Yamma, kuma Sanata Barau Jibrin shi ne zai rike wannan mukamin.

A Majalisar wakilai kuma an ba shiyyar Arewa maso Yamma inda aka zabi Tajudeen Abbas, sannan mataimakinsa zai fito ne daga shiyyar Kudu maso Gabas inda aka zabi Benjamin Kalu.

Hon. Tajudden Abbas
Hon. Tajudden Abbas

Su ma tsofaffin 'ya'yan Majalisar dattawa sun ce suna goyon bayan wannan zabi da uwar jam’iyya ta yi kamar yadda jagoransu Sanata Bashir Lado ya ce tun kafin jam’iyyar APC ta fitar da wannan sanarwa su ke bi su ke yi wa Godswill Akpabio kamfe domin suna ganin shi ne ya fi cancanta da wannan kujerar kuma sun yi farin ciki kwarai da gaske da ganin cewa kiran da su ka yi ya yi tasiri.

Tsofaffin 'Yan Majalisar Dattawan Najeriya
Tsofaffin 'Yan Majalisar Dattawan Najeriya

Sai dai wasu sabbin ‘yan majalisa daga bangaren adawa irin su Inuwa Garba na jam’iyyar PDP daga jihar Gombe, suna ganin ba a yi wa Majalisar adalci ba.

Inuwa ya ce kamata ya yi a yi wa kasa da al'ummarta adalci a bar ‘yan majalisa su zabi wanda su ke ganin ya iya aikin kuma zai hada kan ‘yan majalisa tare da yi masu wakilci mai ma'ana a bangaren zartarwa.

Shi ma dan Siyasa daga jihar Zamfara kuma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum, Annas Abdullahi Kaura, ya yi toskaci cewa Majalisa ta yi tsayuwan daka ta tabbatar da cancanta a harkar zaben shugabanninta, kuma su sa ido sosai domin akwai wadanda ke yi wa jam’iyyar su zagon kasa.

Shiyyar Arewa ta tsakiya dai ta tsira da Sanata Abdullahi Adamu wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC mai mulki.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

Shugabancin Majalisa: Akpabio Da Tajudeen Muke Goyon Baya - APC.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG