Sai dai kuma madugun jam’iyyar adawa ta SDF, John Fru Ndi, yace ba ya sa ran cewa kafa Hukumar zaiyi wani anfani wajen gano abinda ya janyo hatsarin.
A hirar da yayi da gidan rediyon nan na VOA, Ndi ya nemi a kyale wani Kwamiti mai zaman kansa tareda Majalisar Dokokin kasar Kamaru din su gudanarda binciken.
Haka kuma yace bai yarda da alkalumman lissafin mutanen da abin ya shafa da gwamnati ta gabatar ba, inda yace yawan wadanda abin ya shafa ya fi abinda aka fada.
Sai dai kuma a can Yaounde, babban birnin Kamarun, masu goyon bayan gwamnati sunce ba gaskiya a cikin zargin da madugun ‘yan adawar yake yi.