Sanarwar da Babban Sakataren ya bada tace idan har aka tabattarda cewa wannan harin na ganganci, to ya tabatta laifin yaki.
Shima tsohon Fara Ministan Biritaniya Gordon Brown wanda shima manzon musamman ne na MDD kan sha’nin ilmi, ya nemi a yi wannan binciken.
Jiragen saman yaki ne suka kai hare-hare har guda shidda akan wani kauye dake yankin Idlib dake hannun ‘yantawaye, wanda a lokacin ne suka saki bam akan wannan makarantar inda suka hallaka malamai 6 da ‘yan-makarantar su 22, a cewar cibiyar adawar Syria ta “Observatory.”
Da ita cibiyar ta Observatory da fadar shugaban Amurka ta White House dai duk suna dora laifin kan harin ne a kan Rasha ko kuma Syria, amma kakakin ma’aikatar harakokin wajen Rasha, Igor Konashenkov, yace jiragen Rasha basu ratsa sararin wannan yankin a lokacinda aka kai farmakin ba.