Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudin Da Hillary Clinton Ke Kashewa Ya Ninka Na Donald Trump


Hillary Clinton
Hillary Clinton

Yar takara shugancin kasa a nan Amurka karkashin jami’iyar Democrats Hillary Clinton ta ninka abin da abokin karawarta na Republican Donald Trump yake kashewa na zunzurutun kudade a gwagwarmayarsu ta shiga fadar White House.

Amma dai Trump ya fada jiya Laraba cewar zai zuba karin makudan kudaden aljihunsa a cikin yakin neman zabe nasa, a cikin makwanni biyun da suka rage ayi zaben a ranar takwas ga watan gobe ta Nuwamba.

Rahotanni da yan takara suka baiwa gwamnatin Amurka na nuna cewa Hilary Clinton, tsohuwar sakatariyar Harkokin wajen kasar da ta himmantu wurin gani ta kafa tarihin zama macen farko da ta dare a kujerar shugabancin Amurka ta tara dala miliyon 950 kuma har yanzu tana da sauran dala miliyon 178 dake hannu da zata batar wurin tallace tallacen telbijin da kokarin ganin jama’a sun fito sun jefa kuri’unsu.

Shi kuma Donald Trump ya tara dala miliyon 449 ne kuma yana da dala miliyon 97 a hannu.

Trump, wanda hamshakin dan kasuwa mai hada hadar gine gine, jiyaya zo nan Washington don bude sabon Otal dinsa mai cike da alatu wanda ke kusa da fadar White House, kuma ya fadawa gidan telbijin ta CNN cewar ya riga ya kashe kudin aljihunsa dala miliyon dari a cikin yakin neman zabensa.

Wannan dai shine karo na farko da Trump ke shiga zaben rika wani mukkami na siyasa, sai dai yanzu haka yana yana bayan Hilary Clinton a farin jinni gun Amurkawa. Duk da haka Trump ya nace akan cewa shine zai lashe zaben.

To amma masu pashin baki a kan zabe sun ce Hilary Clinton ce ke dada nuna alamun cewa tana dab da yin abin tarihin zama shugabar Amurka ta 45, watau zatamaye gurbin shugaba Barrack Obama wanda wa’adinsa na biyu ke karewa ranar 20 na watan Janairun shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG