Akasarin mutane da wannan hare haren ya rutsa dasu duk yara ne kanana, inji shugaban cibiyar bada agajin, Stephen O’Brien, a cikin rahotonsa na wata wata na aikin kungiyarsa na shiga da kayan agaji ga mazauna yankin da yaki ya daidaita, wanda ya gabatar ga MDD din.
Ya sake maimaita zargi da sakataren MDD da babban komishinan kare hakkin bil adama suka yi a can baya cewa, gwamnatin Syria da Rasha ne ke da alhakin kai hare-haren ruwan bama bamai babu kakkautawa tun farkon wannan yaki da ya barke kusan shekaru shida da suka wuce.
A mako da ya gabata, Syria da Rasha sun fara tsagaita bude wuta a kan gabashin Aleppo na dan lokaci don bada daman fitar da masu tsananin fama da ciwo da masu rauni kuma ma’aikatar agaji su samu daman raba kayan agajin a garin wanda rabon da aka kai kayan agaji a cikinsa an kusa wattani hudu.
An tsawaita shirin tsagaita wutar har zuwa kwanaki takwas, amma rashin samun tabbacin tsaro daga bangarorin masu fada da juna, yasa kungiyoyin bada agajin suka kasa iya shiga su yi aikinsu.