A bangare guda akwai masu kiran kansu APC akida da ke ikrarin ba a bin akidar da aka kafa jam’iyar a kai wanda ya hada da Sanata Sani Shehu, yayin da a bangare guda akwai wadanda ake gudanar da mulkin da su a wannan gwamnati.
Ya zuwa yanzu bangaren APC akida ya gudanar da wani taro inda wasu daga cikin gaggan jam’iyar a jihar suka halarta domin neman mafita.
“Ita jam’iyar APC an kafa ta ne da nufin taimakon talakawa daga mulkin danniya na mulkin da ya gabata, saboda haka akan wannan akida mu ka tsaya mu ke kiran kuma a dawo kanta. Akwai wasu abubuwa da ake yi a gwamnatin Kaduna, wadanda sun sabawa akidar jam’iyar APC.” Inji Mataimaki Tom Mai Yashi da ke bangaren APC akida.
Sai dai a bangaren mukaddashin sakataren yada labarai na jam’iyar ta APC a jihar Kaduna, Alhaji Salisu Tanko Solo, ya ce akwai alama mahalrta taron ba su san kundin tsarin mulkin jam’iyar ta APC ba.
Domin jin dalilin da ya sa ya fadi haka, da kuma jin cikakken rahoton kan wannan takaddama ta jam’iyar APC a jihar Kaduna, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Isa Lawal Ikara: