Shugaban wanda ya nanata ware wasu makudan kudi a kasafin kudi dan tallafawa matasa masu sana’oi da mata ‘yan kasuwa, y ace sai jama’a sun yi hakuri kafin a sami shawo kan matsalolin kasar da kuma rage dogaro ga man fetur.
Saminu Azare wani dan jarida ne a birnin Abuja da ya saurari jawabin shugaban kuma ya yi Karin bayanin cewa wajibi ne a yi wa tattalin arzikin kasar garambawul saboda da talakawa su rage yawan talaucin da ya addabe su a cikin al’umma domin kuwa su suka zabi gwamnatin da kansu, dan haka ya zama wajibi ne gwamnatin ta share masu hawaye.
Da suke hira da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya, dan jaridar ya bayyana ra’ayin sa akan cewar bai kamata ana ba wasu jahohi makudan kudade fiye da wasu ba saboda suna da albarkar man future tunda arzikin kasa ne baki daya.
Masanin tattalin arziki daga birnin Abuja Malam Abubakar Ali ya yi Karin haske inda ya ce “idan kida ya canza, kamata rawa ma ta canza, domin kuwa akwai jahohi da kananan hukumomin da har yanzu suke biyan albashin bogi, wasu ma harda sunayen jariran da aka haifa ake sa sunayen su cikin wadanda ake biya albashi.
Rahotanni da dama sun bayyana cewa ayyukan kwangiloli sun tsaya a jahohi da dama inda masu bin bashin tsofaffin kwangiloli ke ta faman shiga ofisoshi suna bin kafa, kasuwanni kuma da kayayyakin masarufi sun yi dan Karen tasada, ga kuma watan ramadana ya karato wanda ko ba komi akan sami hauhawar farashin kayan abinci.
Ga rahoton Nasiru Adam el-Hikaya daga Abuja.