A cikin makon jiya ne dai wasu mutanen karamar hukumar suka koka akan yadda ake raba filayen da mutanen suka ce karamar hukumar ta kwace ne daga hannunsu.
Alummomin da lamarin ya shafa sun ce sun gaji filayen ne tun daga kakannin kakanensu.
Amma kwamishanan kula da ma'aikatar filaye na jihar Alhaji Haliru Zakari Jikantoro yace filayen mallakar gwamnatin jihar ne. Ita karamar hukumar Suleja bata samu izinin raba filayen ba.
Kwamishanan yace babu shakka filin mallakar gwamnatin jihar ne. Yace gwamnan jihar ya bada umurni a gyara filayen a yi masu tsari kafin a rabasu. Amma ita karamar hukumar bata samu izinin gwamnatin jiha ba.
Onarebul Abdullahi Maje mataimakin shugaban hukumar karamar hukumar ta Suleja yace tabbas filin ba mallakar karamar hukumar ba ne.
Yace wasu da suka dade suna noma a wurin suke cewa filin nasu ne. Har ma sun je kotu inda aka yi watsi da bukatarsu. To amma sai suka cigaba da zama wurin. Yayinda jami'an karamar hukuma masu kula da wurin suka je sai aka farmasu har aka jikata wasu.
Ga karin bayani.