Kamfanin da aka dorawa alhakin gurbata muhallin ya halarci taron gyara yankin da aka yi a karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo tare da bada tabbacin zai taka rawar gani wurin gudanar da aikin.
Bayan jawabai daban daban ministar muhalli ta kasa Hajiya Amina Muhammad ta gabatar da nata jawabin. A cikin jawabin nata ta tabbatar wa mutanen yankin cewa daga jiya an fara aiki gadan gadan ke nan na gyra yakin har sai an gama. Tace shugaban kasa ya dukufa ya ga ya cika alkawuran da ya yiwa al'ummar yankin.Tace zasu yi aikin kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta umurta.
A nashi jawabin mataimakin shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo yace al'ummomin Ogoni sun dade cikin gurbatacen muhalli tare da shakar gurbatacciyar iska da kuma kamun kifi daga cikin gurbataccen ruwa. Yace yayin yakin neman zabe sun yi alkawarin aiwatar da gyaran yankin.Yace suna cikin yankin domin cika alkawarin da suka dauka.
Farfasa Osinbajo yace aikin na bukatar kamfanonin dake hakar mai su sauya halayensu kan kula da muhalli.
Sanata Bukar Ibrahim tsohon gwamnan Yobe wanda ya kasance wurin taron yace ya yi kyau domin an dade ana son gyara muhallin yankin.
Ga karin bayani.