Mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Mongunu shi ya kaddamara da 'yan kwamitin binciken kwakwaf akan sace 'yan matan Dapchi.
'Yan kwamitin zasu duba tsarin tsaro a garin Dapchi musamman a makarantar sakandaran 'yan matan kafin a sacesu. Kwamitin ya binciki yadda naurorin sadarwa ke aiki a garin. Kwamitin ya binciki yadda aka sace daliban kuma su nawa ne aka sace.
Kwamitin zai zayyana yada za'a ceto 'yan matan a koina suke a duniya. An jaddadawa masu binciken cewa su dauki aikin da matukar mahmmanci.
Malam Kabiru Adamu kwararre akan sha'anin tsaro a Najeriya ya ce akwai matsala da nadin kwamitin. A cewarsa irin binciken da kwamitin zai yi kamata ya yi a fadadashi a shigar da jami'an tsaro masu zaman kansu. A sa 'yan jarida masu zaman kansu saboda su ne basu da bangaranci ko siyasa.
Shi ma Sardaunan Damaturu Alhaji Bello Arabi cewa ya yi an taba kafa kwamiti irin wannan akan 'yan matan Chibok amma har yanzu babu wanda ya san sakamakon binciken. A cewarsa wannan ma gidan jiya za'a koma.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum