Kwamishinan ma'aikatar ilmi na jahar Yoben,Malam Mohammed Amin, ne ya tabbatar da al'kaluman a hira da muka yi da shi ranar Asabar din nan.
Kwashinan ya karyata wasu rahotanni da suke cewa dalibai 105 har yanzu ba'a san ind a suke ba. Yace shi da shugabannin makarantar sakandare dake Dapchin ne suka zauna aka rubuta wannan adadi; dalibai 84. Duk da haka yace suna ma da labarin cewa wasu dalibai kamar uku sun gudu zuwa wani kauye, kuma ya nemi da a tabbatar da sunayen su saboda a tabbatar da wadanda hakikanin gaskiya basa nan.
Kwamishinan Ilmin ya kara da cewa akwai wadan su daliban da suke gidajen iyayen su, amma zuwa yanzu iyayen sunki su fito su tabbatarwa hukuma haka.
Kan ko akwai karin matakan tsaro da hukumomin jahar suka dauka a sauran makarantu da suke yankin, yace ai tun lokacinda aka fara rikicin na Boko Haram suka girke jami'n tsaro da suke sintiri ko shawagi a makarantun.
Kwamishinan na Ilmi yace ai ko ranar da maharan suka dira akan makarantar, akwai jami'an sanda a wurin.
Facebook Forum