Bayan da Rundunar Sojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa, inda ta nemi nisanta kanta daga wannan batu na sace wadannan dalibai. Sanarwar da ke dauke da sa hannun mataimakin darektan hulda da jama'a na rundunar sojin kasar karkashin Operation Lafiya Dole, Kanal Nwachukwu Onyema na nuni da cewa, rundunar ta kammala aikinta a wannan gari na Dapchi sannan ta dankawa jami'an 'yan sandan jihar rangamar kulawa da garin kafin suka kwashe suka tafi wani wurin don ci gaba da yaki da ta'addancin Boko Haram.
Sai dai 'yan sandan garin sun musanta wannan batun, inda suka ce babu lokaci guda da soji ta mika musu ragamar kula da wannan gari, sanarwar da ke dauke da sa hannun kwamishinan 'yan sandan Jihar Yobe, Saminu Abdulmalik.
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan sanarwar ta Rundunar Sojin Najeriya ta ja hankalin jami'an 'yan sandan kasar domin a cewarsa, ba gaskiya bane. Ya shaida cewa har yanzu Jihar Yobe na cikin dokar ta bace kuma soji na ci gaba da kokarin maido da zaman lafiya da doka da oda a wannan yanki.
Domin haka ne ya ke bukaci jama'a da su yi watsi da wannan sanarwar ta Jami'an Soji da ke nuni da cewa ta mika garin Dapchi ga 'yan sanda.
Kwamishinan ya kara da cewa, 'yan sanda za su ci gaba da aiki da sauran takwarorinsu na jami'an tsaro domin tabbatar da sun kare lafiya da dukiyar jama'a a jihar Yobe.
Kwana 9 kenan tun da sace wadannan dalibai mata daga makarantarsu kuma har yau babu wanda ya san makomarsu. Gwamnati ta tabbatar da adadin daliban da aka sace da cewa sun kai 110.
Saurari rohoton Haruna Dauda Biu
Facebook Forum