Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Harin Dapchi


Dakin kwanan dalibai mata a makarantar sakandare da ke Dapchi jihar Yobe
Dakin kwanan dalibai mata a makarantar sakandare da ke Dapchi jihar Yobe

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin mutane 12 da za su binciki yadda lamarin sace dalibai 110 daga makarantar kwana ta kimiya da fasaha (GGSTC) a garin Dapchi Jihar Yobe bayan harin da tsagerun Boko Haram suka kai a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018.

Mai baiwa shugaba shawara dangane da tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya ne ya kaddamar da wannan kwamitin.

Wani Manjo Janar na rundunar soja ne zai jagoranci kwamitin da aka kafa, wanda zai hada da manyan jami’ai daga rundanar soji ta kasa, da na sama da na ruwa da wasu daga ma’aikatar tattara bayanan sirri ta NIA.

Sauran sun hada da Sashen leken asiri na soji (DIA) da rundunar ‘yan sanda, da ‘yan sandan farin kaya da kungiyar da ke samar da tsaro ga fara hula ta NSCDC da mutane biyu daga gwamnatin Jihar Yobe da kuma wani daga ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa (NSA).

Kwamitin za su bincike yadda lamarin ya auku, don tabbatar da yanayin tsaro a Dapchi da makarantar kafin harin, wato ya adadin jami’an tsaro da kuma karfinsu ya kasance sannan su kawo matakan da ya kamata a dauka don gano inda yaran suke aka kuma cetosu.

Ana sa ran kwamitin zai gama hada rohoton da ake bukata a ranar 15 ga watan Maris na 2018. Haka zalika kwamitin zai bayar da matakan da ya kamata a dauka don ganin wannan lamarin bai sake aukuwa ba.

Za a kaddamar da kwamitin gobe Laraba, 28 ga watan Fabrairu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG