Bayan da aka yi kwanaki da dama babu wani bayani daga bakin jami'ai, a jiya lahadi, gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da bacewar yara ‘yan mata su 110, a bayan harin da 'yan Boko Haram suka kai kan wata makarantar sakandaren 'yan mata dake garin Dapchi a Jihar Yobe.
Ma'aikatar yada labarai ta ce wannan adadi na ‘yan matan makarantar sakandaren kimiyya da fasaha ta mata dake garin Dapchi a cikin jihar Yobe, sune wadanda aka gaza samun wani bayani game da su bayan wadanda ake tuhumar cewan ‘yan ta'addar Boko Haram ne sun kai musu hari a daren litinin din da ta gabata.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fada jiya lahadi cewa an kara yawan jiragen yaki da sojojin da zasu yi aikin nemo wadannan yaran.
Mayaka dauke da makamai sun kutsa cikin garin na Dapchi da maraicen litinin, inda aka ce sun yi ta tambayar hanyar zuwa makarantar wadannan yaran.
Da farko dai mahukumta sun karyata cewa an sace 'yan matan, su na masu cewa yaran sun buya ne a cikin daji a lokacin da aka kai musu harin.
Facebook Forum