Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Saman Najeriya Da Ma'aikatansu Su Na Iya Zuwa Amurka Kai Tsayea Daga Yanzu


Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka ta ce kamfanonin jiragen saman Najeriya su na aiki da ka'idojin kasashen duniya na kula da jiragensu.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta tarayya ta Amurka ta ba da Najeriya maki mafi girma da ta ke iya bayarwa, abinda ke nufin cewa a yanzu kamfanonin jiragen saman Najeriya zasu iya tasowa kai tsaye zuwa Amurka da jiragensu na kansu da kuma ma'aikatansu.

Jiya litinin hukumar ta FAA ta ce Najeriya tana aiki da ka'idojin kula da lafiyar jiragen sama wadanda duniya suka yi na'am da su.

Wannan hukumcin da hukumar ta Amurka ta yanke ya shafi kamfanonin safarar jiragen saman Najeriya ne kawai. Wannan bai shafi yadda ake binciken fasinjoji ko kuma gudanar da tsaro a filayen jiragen saman Najeriya ba.

Jiragen Saman Najeriya Da Ma'aikatansu Su Na Iya Zuwa Amurka Kai Tsayea Daga Yanzu
Jiragen Saman Najeriya Da Ma'aikatansu Su Na Iya Zuwa Amurka Kai Tsayea Daga Yanzu

Wannan sanarwa ta zo watanni takwas a bayan da aka zargi wani saurayi dan Najeriya da kokarin tarwatsa wani jirgin saman fasinja na Amurka da ya doshi birnin Detroit a ranar Kirsimeti a bayan da ya boye nakiya karkashin suturarsa.

Fasinjoji da ma'aikata sun danne Umar Farouk Abdulmutallab a cikin jirgin suka rike shi a lokacin da suka ga ya tayar da wuta. Abdulmutallab ya taso ne daga filin jirgin saman Lagos, inda jami'ai da na'urorin dake can suka kasa gano nakiyar da ya boye a jikinsa.

XS
SM
MD
LG