Dan Najeriya da ake tuhuma da kokarin tarwatsa wani jirgin saman da ya taso daga Amsterdam zuwa birnin Detroit dake Jihar Michigan a Amurka a ranar Kirsimetin bara, ya sallami lauyoyinsa, ya kuma nuna alamun cewa zai amsa wasu daga cikin laifuffukan da ake tuhumarsa da aikatawa.
A lokacin da Umar Farouk Abdulmutallab ya bayyana jiya litinin gaban kotu a Detroit, mai shari’a Nancy Edmunds ta gargade shi game da hatsarin dake tattare da matakin cewa shi zai wakilci kansa a shari’ar, ta kuma tambaye shi ko me ya sani game da dokokin Amurka. Mai shari’ar tana shirin nada wani lauya na wucin gadi wanda zai ringa ba shi shawara kan shari’a.
Abdulmutallab yana fuskantar tuhume-tuhume shida, ciki har da kokarin yin amfani da makamin kare-dangi, da yunkurin tarwatsa jirgin sama da gangan. Ana zarginsa da kokarin tayar da bam da ya boye cikin kamfansa.
An kama shi ranar 25 ga watan Disambar 2009, bayan da fasinjoji suka taru suka rike shi da suka ga kayan jikinsa na ci da wuta. An yi zargin cewa ya samu horaswa a hannun ‘yan al-Qa’ida a Yemen.