Wani tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya ya ce zai nemi mukamin shugaban kasa a wani mataki na kalubalantar shugaba Goodluck Jonathan wanda ake kyautata zaton zai fito takarar wannan kujera.
Atiku Abubakar, wanda yayi wa'adi biyu kan kujerar mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Olusegun Obasanjo, ya fada jiya lahadi cewa zai nemi zamowa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.
Abubakar ya shiga wannan takara a lokacin da jam'iyyar ta ke muhawara a kan ko za ta kyale Mr. Jonathan ya zamo dan takararta a zaben da za a yi a shekara mai zuwa.
Ana tabka wannan muhawara ce a saboda jam'iyyar ta PDP tana da wani tsari na karba-karba a tsakanin arewaci da kudancin Najeriya. A zaben 2007 jam'iyyar ta tsayar da Umaru Musa Yar'aduwa, Musulmi kuma dan Arewa. Amma daga bisani sai ya rasu bai ma kammala ko wa'adi a kan mulki ba. Daga nan ne Mr. Jonathan, Kirista kuma dan Kudu ya amshi ragamar mulkin kasar.
Shi ma Abubakar, kamar Yar'aduwa, Musulmi ne daga arewacin Najeriya.
Har yanzu Mr. Jonathan bai fito ya ayyana takararsa ba, amma ana kyautata zaton zai yi hakan. A wannan makon, shugabannin jam'iyyar PDP sun ce Mr. Jonathan yana da ikon tsayawa takara, amma ba su a fili sun ce shi ne dan takararsu ba.
A shekarar 2007, Atiku Abubakar ya samu sabani da jam'iyyar PDP a saboda adawar da ya fito yayi da wani shirin yin gyara ga tsarin mulkin kasar ta yadda shugaba na lokacin, Obasanjo, zai iya neman wa'adi na uku a kan karagar mulki. Yayi takara a zaman dan hamayya a lokacin, ya zo na uku.
Yace a wannan karon zai yi takara a inuwar jam'iyyar PDP. Amma jam'iyyar ta ce har yanzu ba a gama shigar da shi a zaman cikakken memba ba.
Shi ma tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja Ibrahim Babangida ya ce zai yi takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa. Babangida ya hau mulki a bayan juyin mulki a 1985, amma daga bisani an tilasta masa ya sauka a bayan da gwamnatinsa ta soke wani zabe a 1993.