‘Yansandan Najeriya sun tsare wani tsohon shugaban wani Banki da ake zargi da aikata raashin gaskiya,bayan ya koma kasar daga Ingila.
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa, EFCC, sun ce jiya laraba ce suka kama Mr. Erastus Akingbola,tsohon shugaban Bankin Intercontinental,kuma ana masa tambayoyi.
Cikin watan Agustan bara ne Mr. Akingbola ya gudu zuwa Ingila bayan da babban Bankin Najeriya ya kore shi daga bakin aiki,kuma ya tuhume shi, da wasu takwarorin aikin sa hudu, da laifin sata da kuma halatta kudaden haram.