Nijeriya ta ce za ta sayo sabbin jiragen sama kirar jet-jet wa Shugaban kasar, a daidai lokacin da kasar ke kokarin neman kudin fara shirin zabe mai zuwa da kuma farfado da bangaren wutar lantarki.
Ministar Yada Labarai, Madam Dora Akunyili, ta fadi yau Laraba cewa Majalisar Ministoci ta bayar da umurnin sayo jiragen sama samfurin Falcon 7X guda biyu daga kasar Faransa da kuma sanfurin Gulfstream G550 guda daya daga Amurka. Za su lakume wajen dala miliyan 150.
Akunyili ta ce dama an samar da kudin a kasafin kudin 2010 na Nijeriya.
Jiya Talata, Yan Majalisar Tarayyar Nijeriya su ka bada izini a takardance, wanda zai bai wa gwamnati damar aro kudi, don ta hada dala miliyan 585 don shirin babban zaben 2011.
Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma yi alkawarin gina sabuwar tashar wutar lantarki da za ta ci dala miliyan dubu 3 da dari biyar don inganta fannin samar da wutar lantarki. Ya ce da gwamnati ne da yan kasuwa da cibiyoyin cinakayya da kawo cigaba na kasa da kasa za su dau nauyin.