Bayana na nuni da cewa, kananan yara sittin da biyu suka kamu da cutar shan inna a Najeriya, yayinda kawo yanzu aka tabbatar da yara masu dauke da cutar a jihohi takwas na arewacin kasar.
A shiyar arewa maso gabas an sami bullar cutar a jihohin Yobe da Borno da Bauchi bana. Ta dalilin haka, gwamnatin jihar Yobe ta kara kudin da ta kiyasta na yaki da cutar daga naira miliyan shida zuwa miliyan goma bayan gabatar da wadansu sababbin shirye domin yaki da cutar.
Mataimakin gwamnan jihar Injiniya Abubakar Aliyu wanda kuma shine mai sa ido kan ma’aikatar lafiya ta jihar ne ya bayyana haka jim kadan bayan wani taron polio a jihar.
Mataimakin gwamnan yace za a kara kaimi wajen fadakar da iyaye wadanda suke shakkun bari a yiwa ‘ya’yansu rigakafin. Ya kuma bayyana muhimmancin ‘yan jaridu a cimma nasarar wannan yunkurin.
Injiniya Aliyu ya yi kira ga shugabanni su kara himma wajen ganin an shawo kan cutar yayinda yayi kira ga al’umma su rika bari ana yiwa ‘ya’yansu alular rigakafin yayinda kuma ya shawarce su rika tsabtace muhallinsu.