Kasar Ghana ta zama ta farko a nahiyar Afrika da ta fara amfani da wani sabon maganin rigakafin kananan yara, da aka samar da nufin shawo kan matsalar gudawa da cutar namoniya dake katse hanzarin sama da kananan yara miliyan biyu da dubu dari biyar kowacce shekara a duniya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rigakafin, ministan lafiya na kasar Ghana Alban Bagbin yace shirin wata babbar ci gaba ce. Bisa ga cewarshi, kananan yara sun dade suna mutuwa da cutukan da ake iya magancewa.
Ministan ya ci alwashin cewa, aiwatar da wannan shirin rigakafin hadi da rigakafin shan inna da ake gudanarwa a halin yanzu, kasar Ghana ta hakikanta cewa zata rage mutuwar kananan yara da ake yi da kimanin kashi biyu bisa dari nan da shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.
Babban jami’in cibiyar rigakafi ta duniya da ake kira “Global Alliance for Vaccines and Immunisation.”, cibiyar da ta bada tallafi a shirin, Dr Seth Berkly ya bayyana cewa, an sami nasarar kaddamar da maganin rigakafin ne sakamakon ingancin dakunan jinya da ake da su a kasar Gahana da kuma issashen maganin rigakafi hadi da gagarumin tallafin kudi daga kasa da kasa .