Wannan kuri’a ta kuma gano cutar Typod da zazzabin cizon sauro sune manyan cututtukan da yawancin marasa lafiya (kashi 50%) suka karbi maganin su daga hannun jebun likitoci, daga nan kuma sai maganar ciki da kuma haihuwa (kashi 11%).
Hakanan kuma, masu yin bayani sun baiyyana cewa lafiyar marasa lafiya na kara lalacewa bayan wannan maganin. Wannan shine sakamakon babban binciken da akayi a satin Janairu 13, da ya shafi ma’aikatan lafiya da basu kware ba wanda aka baiyyana a Abuja ranar Talata.
Ruhotanni na kwanannan a Nijeriya sun nuna karuwar likitocin jebu, wanda ke da matsala ta jiki ga rayuwar mutane da kuma tsawon shekarun ‘yan Nijeriya.
A shekara ta 2013, an sami ruhoton kame-kame da ‘yan sandan Nijeriya sukayi a jihohi da dama, musamman jihar legas. A misali, kungiyar likitoci ta Nijeriya ta jihar Rivers ta ‘yan sanda su kama jebun likitoci 12 kuma rufe asibitocin da aka bude ba bisa ka’ida in ji binciken.
Kungiyar binciken ta lura da cewa duk da kasafin kudin shekara da gwamnatoci keyi domin lafiya, har yanzu wannan sashi na fama da kalubala iri dabam dabam: rashin isassaun kudade domin sashin lafiya; ingancin likitoci dake fita daga makarantun kiwon lafiya; rashin kyawawan kayan aiki; da kuma rashin biyan gamsasshen ladan aiki ga ma’aikata, dukan wadannan na kawo yawan yajin aiki, wanda ke ma’aikatan kiwon lafiya damar baje kolinsu. NOIPolls tayi ma yadda aikin wadannan mutanen ya ke shafar kiwon lafiya a kasar.
Bincike daga wannan kungiya ya nuna cewa yawan wadanda suka bada bayani (kashi 79%) sun bada amsar cewa suna sane da karuwar likitocin jebu a nijeriya, sai kuma kashi 21% na ‘yan Nijeriya suka nuna basu sani ba.
Karin bincike ya nuna cewa yawancin masu bayani (kashi 44%), suna da fahimtar cewa likitocin jebu mutane ne marasa cikakkar kwarewa; kuma kashi 35 na masu bayani sun yarda cewa “mutane ne da suke nuna kamar sun kware a aikin magani”.