Da yammacin jiya Litinin, an ayyana Kyrsten Sinema, a matsayin wadda ta lashe zaben kujerar Sanata daga jihar Arizona, wadda ta doke abokiyar takararta ‘yar jam’iyyar Republican Martha McSally da kusan kashi biyu cikin dari na kuri’un da aka kada.
McSally dai ta aikawa Sinema sakon murna da fatan alkhairi ta shafin Twitter.
Sinema za ta zamanto mace ta farko da ta taba zama ‘yar Majalisar Dattawa daga Arizona.
Zaben Arizona na daya daga cikin zabukan sanatocin da ba a san sakamakonsa ba, bayan da aka kammala zaben rabin zango tun ranar Talatar da ta gabata.
Yanzu haka dai ido ya koma kan jihar Florida, inda har yanzu ana can ana ci gaba da kirgan kuri’u na zaben ‘yan Majalisar tsakanin Sanata Bill Nelson na Dimocrats da abokin takararsa Gwamna Rick Scott na Repubican.
Ya zuwa jiya Litinin dai Scott yana kan gaba da kuri’u 12,500. Haka kuma ana sake kirgan kuri’un zaben gwamnan jihar Floridan.
Facebook Forum