A wata hira da manema labarai a garin Gombe, dan majalisar wakilan yace samar da ofisoshin jami'an tsaro. makarantu, cibiyoyin ayyukan lafiya dakuma gina dakunan kwanan mutane nada cikin abubuwan da ya zama tilas a samar dasu kafin a fara mayarda mutane garuruwansu.
A cewar sa ba wai mayar da mutane gidajensu da basu abinci shine kadai aiki ba, domin akwai sauran bukatu na jama’a, kusan duk mutanen da ke cikin wannan hali a baya suna da sana’a idan aka mayar da su yanzu basu da ita, dole ne a tabbatar da cewa an dawo da tattalin arziki a yankunan.
Duk da yake gwamnatin tarayya na cewa an kammala shirye shirye na ganin an fara jigilar ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu domin an fara samun kwanciyar hankula. Alhaji Ali yace tabbas suna goyon bayan jama’a su koma gidajen su, idan da akwai gidajen kenan saboda an kone gidaje masu dinbin yawa.
Saurari hirar mataimakin kwamitin samar da agajin gaggawa da manema labarai.