Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaron Nijar Sun Yi Kuskuren Harbe Wani ‘Dan Sanda


Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

Wani ‘dan sanda a Jamhuriyar Nijar ya hadu da ajalinsa a yammacin jiya bayan da jami’an tsaron Jandarma suka bude masa wuta lokacin da ya shiga jami’ar Yamai da daddare dauke da makami cikin wani yanayi mai duhu.

NIAMEY, NIGER - Rashin sanin takamammen dalilin zuwan ‘dan sandan a harabar jami’ar sanye da farin kaya da kuma yadda ya arce da gudu lokacin da Jandarmomi suka bukaci ya tsaya, ya sa suka bude masa wuta lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa a take, kamar yadda Sakataren kungiyar daliban jami’ar Abdoul Moumouni Dofo a Yamai Almoustapha Bakin Batoure ya shaidawa Muryar Amurka ta waya.

A cewar wasu bayanai ‘dan sandan mai suna Issa Ibrahim ya tafi jami’ar ne domin tattaunawa akan wata magana da daya daga cikin shugabaninta suka bukace shi, to amma rashin jittuwar da aka samu a tsakaninsa da wasu ‘dalibai ya sa suka bukaci dauki daga jami'an tsaron Jandarma da ke aikin tsaro a kewayen jami’ar.

‘Daliban na zargin yiyuwar wannan ‘dan sandan dan ta’adda ne da ya ke kokarin shiga jami’ar domin tafka ta’asa.

Lokacin da ya ga Jandarmomi sun iso sai ya fita da gudu lamarin da ya sa suka harba bindiga a sama a matsayin kashedi amma bai tsaya ba, dalili kenan suka bindige shi har lahira.

Kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani game da wannan al’amari ba.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Jami’an Tsaron Nijar Sun Yi Kuskuren Harbe Wani ‘Dan Sanda.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG