Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51

Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13
Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13

Gwamnatin Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar tallafin wasu motoci 51 wadanda darajarsu ta haura million 13 na dolar Amurka domin tallafa ma jami’an tsaron kasar a yakin da suke kafsawa da kungiyoyin ta’addancin Yankin Sahel.

NIAMEY, NIGER - Wannan tallafi na gwamnatin Amurka ya kunshi motoci kirar Toyota Foker kimanin 43 don amfanin askarawan rundunar yaki da ta’addanci mai sansani a Ouallam da ke Jihar Tilabery da rundunar dakarun musamman ta Force Speciale da ke Tilia a Jihar Tahoua wadanda ke yaki da kungiyoyin ta’addanci akan iyakar Nijar da Mali da kuma iyaka da Burkina Faso. Sai kuma wasu dankara dankaran motocin yaki masu sulke samfarin M36 kimanin 8 domin aikin tabbatar da tsaro a Ouallam.

Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13
Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13

Jami’ar diflomasiyar Amurka a Nijar, Madame Suzane N’garnim ita ce ta damka wa hukumomi wannan tallafi.

Ta ce dukkanmu mun san yanayin tsaro a kasar Mali ya na cikin halin tangal-tangal, wajen kare iyakokinta 7 kasar Nijar na aika dakarunta zuwa kasashen waje domin aikin wanzar da zaman lafiya a baki dayan wannan yanki.

Al’ummomin yankin Sahel na samun kwarin gwiwa ta dalilin sojojin da Nijar ke aikawa zuwa Mali ne, saboda haka gwamnatin Amurka za ta ci gaba da ba ku gudunmowa ta hanyar horo da abin da ya shafi ayyukan hadin gwiwa.

Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13
Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13

Da yake karbar wannan tallafi Ministan tsaro Alkassoum Indatou ya bayyana cewa, "muna godiya kwarai ga kasar Amurka saboda yadda take ba mu tallafi akai akai domin tsaron al’ummarmu, muna fatan rundunonin mayakan sauran kasashe za su yi koyi da irin ta mu wajen jajijrcewar akan maganar tsaron kasa kamar yadda ita ma ta fada cewa muna ba kasashe makwafta dauki a yaki da ‘yan ta’adda saboda wannan yaki ba na kasa guda ba ne abu ne da ya shafi dukkan kasashe."

Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13
Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Sama Da Miliyan 13

A yanzu haka wasu sojojin Nijar da suka kammala daukan horo akan dubarun yaki da ta’addanci na shirin zuwa kasar Mali domin aikin wanzar da zaman lafiya saboda haka za a yi amfani da wani bangare na wannan tallafi a wannan kasa.

Saurari cikakken rahoton daga Souley Moumouni Barma:

Gwamnatin Amurka Ta Bai Wa Jami’an Tsaron Nijar Tallafin Motoci 51 Masu Darajarar Miliyan 13 .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

XS
SM
MD
LG