Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Cafke Wani Dan Kungiyar Farar Hula Da Shugaban Wata Jam'iyyar Hamayya


Ouhoumoudou Mahamadou
Ouhoumoudou Mahamadou

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun kama shugaban kungiyar kare muradan jama’ar jihar Tilabery da shugaban wata jam’iyyar hamayya saboda zarginsu da furta kalaman da ke barazana ga zaman lafiya, sai dai wasu ‘yan fafutika na daukar matakin a matsayin bita da kullin siyasa.

A sanarwar da suka fitar a karshen mako a karkashin inuwar kungiyar da ake kira Comite Union Tilabery pour la paix la securite et la cohesion sociale, dangane da yanayin tsaron da ake ciki, ‘yan asalin jihar Tilabery mazauna birnin Yamai sun zargi Faransa da Chadi da shirin yin aika aika a kasashen Burkina Faso da Mali da gamin bakin hukumomin Nijar, kamar yadda Amadou Harouna Maiga shugaban kungiyar ya bayyana.

Harouna ya ce, kwamitin hadin kan Tilabery ya yi Allah wadai da matakin girke sojojin Faransa a gundumomin Tera da Ayerou, wadanda ke cikin shirin kai farmaki akan iyakokin Burkina da Faso da Mali ta bangaren Nijer. Wannan matakin girke dakaru wani yunkuri ne na shirin kai hare hare kan wadannan kasashe aminan Nijar, wasu bayanai da ke yawo sun nuna cewa an gano sojan hayar Chadi tare da sojojin Faransa cikin shirin ko-ta-kwana a yankin da ake yi wa lakanin yankin iyakoki uku.

Wadannan kalamai dai ba su yi wa hukumomin Nijar dadi ba, mafari kenan jami’an tsaron farin kaya suka cafke shugaban kwamitin na Union Tilabery Amadou Harouna Maiga a yammacin ranar Talata 2 ga watan Mayun 2023.

A wata sanarwar da aka tura wa manema labarai, ofishin Firai Ministan Nijar ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci irin wadannan zarge zarge marasa tushe ba, da ake son fakewa da ‘yancin fadin albarkacin baki ko na kungiya wajen yada su. Haka kuma ba za iya labewa da hujjar neman zaman lafiya ba don furta irin wadannan munanan kalamai da nufin bata suna da kimar kasa wanda kuma yunkuri ne na neman haddasa husuma a tsakanin Nijar da makwaftanta da ma kasashen duniya baki daya. Dalili kenan gwamnati ta yanke shawarar shigar kara a kotu domin gudanar da bincike ta yadda za a hukunta dukkan masu hannu a wannan al’amari inji sanarwar, a cewar sanarwar.

Nadin shugaban ma’aikatar Douane ko kuma Costum da majalissar ministoci ta sanar a makon jiya ya fuskanci suka daga shugaban jam’iyyar adawa ta SDR Saboua Kane Habibou Kadaoure, wanda a shafinsa na Facebook ya rubuta cewa “badaway” ma’ana mutanen daji sun fara samun manyan mukamai.

Ganin yadda jama’a suka yi masa ca ya sa ya nadi murya ta manhajar WhatsApp domin fayyace abinda rubutunsa ke nufi.

To amma wannan bai wanke shi ba daga rubutun kabilancin da ake zargin ya yi a shafinsa na Facebook, ‘Yan sanda suka kama shi a jiya Talata. ‘Yan rajin kare hakkin jama’a irinsu Maikoui Zody na Tournons La Page, na ganin matakin hukumomin tamkar wani yunkuri ne na hana ‘yan kasa morar romon dimkoradiyya.

Kawo yanzu makusanta ko lauyoyin wadannan mutane ba su fito suka yi bayani dangane da wannan al’amari ba.

Saurari cikakken rahoton Souley Mumuni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG