Yau Jam’iyyar PDP ke gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamnonin jihohin kasar. Sakamakon zaben shi ne zai bayyana mutanen da za su yi wa Jam’iyyar takarar gwamnoni a zabe mai zuwa. Sai dai a jihar Kano bangarori biyu ne na Jam’iyyar ke gudanar da zaben a wurare mabanbanta.
Mutane 9 ne dai ke bukatar Jam’iyyar ta PDP ta tsayar da su takarar gwamnan jihar Kano kuma sune ke fafatawa a zaben nay au.
Masu bukatar takarar sun hada da Dr. Yunusa Adamu Dangwani da Yusuf Bello Danbatta da Al’amin Ibrahim Litile Muazu Magaji da Muhuyi Magaji da Jaafar Sani Bello da Mustafa Getso da kuma Mohammed Abacha.
Sai dai ga alama, kamar sauran zabukan da PDPn tayi a Kano cikin karshen makon jiya wanda har yanzu ba’a kai ga bayyana sakamakon sa ba, zaben yana cike da rudani laka’ari da cewa, bangarori biyu dake ikirarin shugabancin jam’iyyar a Kano kowanne zai gudanar da nasa zaben.
To amma Alhaji Mohammed Ibrahim Attah, shugaban kwamitin riko na PDP wanda shalkwatar Jam’iyyar ta turo daga Abuja yace su kuma suna shirya nasu zaben ne a cibiyar koyawa matasa sana’o’i ta Sani Abacha dake kan hanyar Madobi.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda zaben zai kaya da kuma bangaren da ‘yan takarar za su karkata domin neman kuri’a, kana kuma ko sakamakon wane bangare ne uwar Jam’iyya zata karba domin mikawa hukumar zabe ta kasa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari: