PDP dai wadda ke aikin tantance ‘yan takarar ta tace ta dauki matakin ne saboda samunsu da gazawa wajen cika ka’idojin jam’iyyar da suka hada da rashin biyan haraji da kuma rashin cikakkun takardun kammala makaranta.
PDP dai na aikin tantance ‘yan takarar ne a dai dai lokacin da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta bada shawarar yin gwajin shan miyagun kwayoyi ga ‘yan takarar domin kaucewa tsaida ‘yan kwaya wajan neman mikami.
Sanata Mustapha Sani tsohon dan Majalisar Dattawan Najeriya ne da PDP ta tantance ya ce hakan shawarace mai kyau.
Suma dai wasu ‘yan takarar da suka samu nasarar tsallake tantancewa a PDP suna ganin yin hakan na da amfani.
A yanzu dai dukkanin Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun dauki harama domin ganin a fafata dasu a zaben na badi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: