Babbar jam’iyyar adawa ta Peoples’ Democratic Party a Najeriya (PDP) ta ce dalilin da ya sa ta yanke shawarar kin mika tikitin dan takarar shugaban kasa ga wani yanki shi ne, don a tabbatar da adalci.
PDP ta kai ga cimma wannan matsaya ce a karshen taron majalisar zartarwar jam’iyyar da ya wakana a daren ranar Laraba a Abuja a karo na 96.
“Bayan tattaunawa da aka yi mai zurfi, majalisar zartarwar jam’iyyar PDP ta yanke shawarar a bar kofar neman tikitin takarar mukamin shugaban kasa a bude.
“Majalisar zartarwar ta bi shawarar da kwamitin da aka kafa don duba wannan batu, wanda ya ba da shawarar a yi hakan saboda a tabbatar da adalci da ba da dama ga kowa da kowa.” Wata sanarwa da taron ya fitar dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Hon. Debo Ologunagba ta ce.
Jam’iyyar har ila yau ta bayyana cewa daga ranar 28 zuwa 29 ga watan Mayu za ta gudanar da babban taronta na kasa a Abuja inda za ta tsayar da dan takarar shugaban kasanta.
‘Ya’yan jam’iyyar da suka fito daga yankin kudancin Najeriyar sun yi ta hankoron ganin an ba yankin damar fitar da shugaban kasa, lamarin da ya ci tur.
Taron na PDP ya kuma kafa kwamitin da zai jagoranci babban gangamin jam’iyyar na kasa, inda aka zabi Sanata David Mark a matsayin Shugaba kwamiti, sai Hon. Ifeanyi Ugwuanyi a matsayin mataimakinsa da kuma Barrister Ibrahim Shema a matsayin sakataren kwamitin.
“Za mu tabbatar da an yi adalci tare da gudanar da sahihin zabe don zabar ‘yan takarar da za su wakilici jam’iyyar a zabuka daban-daban a babban zaben 2023.”