Ita dai kungiyar al-Shabab ta fada jiya Litinin cewa sojojinda ta kashe talatin ne yayinda rundunar sojojin kasar kuma tace akalla sojoji 15 ne 'yan ta'adan suka kashe.
Haka kuma 'yan yakin sa kansun ce sun kwace motocin soja da dama a kwantar baunar da suka yi.
Sun yi kwantar baunan ne a wani wuri mai tazarar kilomita 100 kudu da Mogadishu babban birnin kasar.
'Yan al-Shabab sun kai harin ne kwana daya bayan da suka kashemutane 12 a wani otel a birnin Mogadishu.
Wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da harinda aka kai otel din suka kuma jaddada kudurinsu na goyon bayan gwamnatin kasar a yunkurin da take yi na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Sun kara da cewa hare-haren ta'adanci da 'yan al-Shabab ke kaiwa ba zasu kassara aniyar da suka kudurta ba