Harin ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 12 ciki har da mai otel din da wani kwamandan soji da kuma wasu 'yan majalisar dokoki biyu.
Kwamitin Sulhun ya yaba da matakin da sojojin Somaliya su ka dauka, wanda ya kai ga kashe dukkannin maharan, ya na mai jaddada cewa ta'addanci, a dukkannin nau'ukansa, na daya daga cikin abubuwan da su ka fi yin barazana ga kwanciyar hankali a duniya.
Hukumomi sun ce mayakan sun tayar da bama-baman aka shake cikin motoci a mashigar otal din na Sahafi, sannan 'yan bindiga su ka abka cikin otel din, wanda jami'an gwamnati da manyan 'yan kasuwa su ka fi sauka.
Ministan Tsaron Somaliya, Abdulrazak Omar Muhammed, ya gaya ma Muryar Amurka cewa maharan na sayen ne da kakin sojin kasar Burundi, wadanda ya ce watakila sun samu ne yayin da Al-Shabab din ta kai wani mummunan harin kan sansanin sojojin Burundi din da ke Leego a cikin watan Yunin wannan shekarar.
Cikin wadanda aka kashe har da Janar Abdulkarin Yusuf Dhagabadan, wani tsohon kwamandan sojoji wanda ya jagoranci samamen da ya tilasata ma Al-Shabab ficewa daga Mogadishu a watan Agustan 2011.
A baya Janar Dhagabadan ya yi ta tsallake rijiya da baya a yunkurin Al-Shabab na kashe shi.
Kakakin Al-Shabab Sheihk Abdul'aziz Abu-Musab ya ce su su ka kai harin a wani bayanin da ya fitar jiya Lahadi.