Wadanda 'yan tawayen suka cafke makon jiya 'yan kwangila ne dake yiwa majalisar aiki suna raka jirgin man fetur da ake shigo dashi ta kogin nilu.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi daga hedkwarta dake Sudan ta Kudu majalisar tace ta dauko 'yan kwangilan kuma an maido mata da jirgin daukan man.
Tun farko majalisar ta kira 'yan tawayen wadanda bangaren SPLA ne dake adawa cikin kungiyar su sako 'yan kwangilan tare da litan man fetur 55,000 da kayan sadarwa da makamai bakwai da suke cikin jirgin da 'yan tawayen suka cafke ranar 26 ga watan jiya.
Yayinda suka cafke jirgin 'yan tawayen sun tsare wasu ma'aikatan wanzar da zaman lafiya su 18 amma an sakesu bayan kwana uku.
Yayinda wani jami'in majalisar dinkin duniyan ke magana yace kodayake muna murna da sako ma'aikatanmu ya kamata mu sake jaddadawa wadanda suke fafatawa da junansu a Sudan ta Kudu su kiyaye dokokin kasa da kasa akan ma'aikatan majalisar. Dole ne a basu damar shige da fice ba tare da tsangwama ba ko yiwa rayuwwarsu barazana. Kada a kuskura a bari irin wannan ta'asar da sake faruwa inji wakiliyar majalisar a kasar EllenLoej.
Majalisar Dinkin Duniya tana da ma'aikata 13,000 da suke aikin kare fararen hula da kuma neman hanyar kawo karshen rikicin da ya barke tun shekarar 2013 tsakanin magoya bayan Shugaba Salva Kiir da kuma masu goyon bayan tsohon mataimakinsa Riek Machar.
Kawo yanzu rikicin ya yi sanadiyar raba mutane miliyan 2.2 da muhallansu da suka hada da 700,000 da suka arce zuwa kasashen dake makwaftaka da kasar