Jiya Linitin Fara ministan Italiya, Giuseppe Conte, ya ce manufarsu itace “su taimaka wajen kawo karshen yakin da ake a Libya da kuma daura kasar kan tafarkin zaman lafiya… ya ci gaba da cewa muna son ‘yan kasar Libya su sami damar zaben abin da suke so.”
Kasar Italiya dai tana da manufa ta musamman akan abubuwan da suke gudana a Libya.
Kasancewar Italiya itace kasa ta farko da bakin haure ke fara zuwa, akan hanyarsu ta shiga Turai daga gabar tekun Libya. Yawancin lokuta kuma masu safarar mutane kan bar jiragensu da suka lalace a tekun Meditaraniya mai hatsarin gaske.
Bayan kwashe shekaru suna neman taimakon kungiyar tarayyar Turai da sauran kasashe, yanzu haka dai gwamnatin Italiya ta rufe tashoshinta ta ga jiragen bakin haure, tana mai tilasta musu su nemi wani wajen sauka bayan kwashe makonni a ruwa.
Facebook Forum