Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 7 Sun Mutu A Wani Fada Da Ya Barke A Kasar Yemen


A jiya lahadi fada ya barke a tsakani 'yan tawayen Houth da kuma Sojojin kawance da Saudiyya kewa jagoranci, inda mutane bakwai suka rasa rayukan su har lahira.

Fada ya barke a titunan kasar Yemen a kusa da muhimmiyar tashar jiragen ruwa ta Hodeidah tsakanin ‘Yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Kasar Iran, da kuma Sojojin kawancen da Kasar Saudiyya ke jagoranta.

Rahotanni sun ce akalla fararen hula bakawai suka mutu a wannan fada.

A jiya Lahadi wani jami’i daga cikin sojoji masu goyon bayan kasar Yemen, ya ce manufofin sojojin shine na kakkabe ‘yan tawaye daga birnin, wanda su ke rike da ikon yankin da tashar jiragan ruwan yake,

A inda ta nan ne kusan dukkan kayan abinci, magunguna da kuma sauran kayayyaki da ake kaiwa fararen hula yake shiga.

Ma’aikatan agaji na fargabar lalata tashar jiragen ruwan, ka iya haifar da yunwa a kasar domin ta nan ne a ke shigar da kayyaki cikin Yemen, wacce ke gab da fadawa kangin matsananciyar yunwa.

Hukumomin Saudiyya na zargin ‘yan Houthis da yin amfani da tashar jiragen ruwan wajen samun makamai daga Kasar Iran, zargin da Iran ta musanta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG