Wani jami'in kasar Isira'ila, yace kasarsa ta yanke shawara cewa ba zata baiwa Palasdinawa dala miliyan ashirin da biyar data karba haraji daga Palasdinawa ba, domin maida martani ga yunkurin da Palasdinawa ke yi na samun wakilci a kotun kasa da kasa da ake cewa ICC a takaice
Palasdinawa na dogara ne akan wadannan kudaden shiga duk wata domin biyan ma'aikata albashi da kuma gudanar da harkokin gwamnati.
Baban mashawarcin Palasdinawa Saeb Erakat yayi Allah wadai da wannan mataki da Isira'ila ta dauka, kuma yace hakan ba zai sa Palasdinawa su karaya a begensu na neman wakilci a kotun ICC ba.
Isira'ila ta dauki wannan mataki ne, kwana daya bayan da Palasdinawa suka mikawa Majalisar Dinkin Duniya takardun niyarta na samun wakilci a kotun ICC, mataki da zai basu sukunin neman a caji Isira'ila da aikata laifuffukan yaki.
Dama kuwa Prime Ministan Isira'ila yayi barazanar daukar matakan da bai baiyana ba, na maida martani ga yunkurin Palasdinawa na neman wakilci a kotun kasa da kasa ICC.