Gobe Talata ce idan Allah Ya kaimu wakilai karkashin jam'iyyar Republican masu rinjaye zasu fara aiki a majalisar wakilai data dattijai, inda masu ra'ayin mazan jiya suka kuduri aniyar rusa manufofin shugaba Barack Obama.
Shugaban masu rinjaye mai jiran gado a majalisar dattijai Mitch McConnell, ya fada a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta CNN jiya Lahadi, yace domin Amurkawa sun zabi jam'iyu daban daban a bangaren majalisa da na zartaswa, hakan ba yana nufin a-yi-jani in-jaka ba. McConnell yace masu zabe suna son sassan biyu su hada kai tare da yin sassauci kan muhimman muradin kasa.
Shugaban na 'yan Republican a majalisar dattijai yace aiki na farko da zasu sa a gaba shine amince da dokar dasa bututun mai daga Canada zuwa Amurka da ake kira Keystone. Masu goyon bayan shirin sun ce aikin zai samar da ayyukan yi kuma ya baiwa Amurka 'yanci kai a banagaren makamashi. Amma 'yan jam'iyyar Democrat masu adawa da shirin suka ce aikin idan har aka gudanar zai kasance bala'i ne da zai shafi muhalli, kuma duk ayyukan d a shirin zai samar na wucin gadi ne in banda kadan daga cikinsu.
Haka nan ana zargin 'yan Republican a duka majalisun guda biyu zasu yi kokarin rusa dokar kiwon lafiya daya daga cikin nasarorin shugaba Obama ya zartas, sannan su hana aiwatar da dokar shugaban kasa da ya bayar kan makomar wasu bakin haure.