Kwana shida kenan Israila na ruwan wuta a Zirin Gaza. A yayin da Majalisar Dinkin Duniya da ma Amurka ke kokarin shiga tsakani a tsagaita wuta, kasashen Larabawa da kasashen Musulmi sun ja bakin su, sun yi gum ba me cewa komi.
A kan haka ne Babban Editan Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha na Sokoto ya tuntubi kwararren masani harakokin yankin Gabas ta Tsakiya, kuma Malamin Addinin Islama, Sheikh Aminu Daurawa na Darul Sunnah Islam Foundation a Najeriya:
Idan ba a manta ba dai Israila ta kaddamar da kai hare-haren kan Zirin Gaza ne bayan kisan wasu matasa uku Yahudawa da ake zargin kungiyar Hamas da aikatawa.
Israila ta ce ta na kai hare-haren ne domin ta kare kan ta daga rokokin da Falasdinawa ke harba ma ta.
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya na kira ga bangarorin biyu da suka kai zukata nesa kuma su tsagaita wuta.