An kammala zaben Zakarun ‘Yan Kwallon Afirka na Muryar Amurka na shekarar 2014. Sakamakon zaben ya nuna cewa ‘yan kwallon Afirka hudu da suka zama zakaru su ne suka fi fice a duk cikin ‘yan kwallon na duniya da aka zaba. Dan Najeriya kuma mai tsare wa Lille gida Vincent Enyeama shi ne ya fi samun kuri’u inda ya samu 2046. Dan Najeriya kuma dan wasan CSKA Moscow Ahmed Musa ya samu kuri’u 1614 kana wani dan Najeriyan dan wasan Fanerbahce Joseph Yobo ya samu kuri’u 1431 sai kuma dan kasar Ivory Coast mai bugawa Manchester City Yaya Toure da ya samu kuri’u 1393.
Wadannan ‘yan wasan hudu suna cikin ‘yan wasan da suka fi kwarewa a duniya cikin watanni 12 da suka gabata. Enyeama, Musa, da Yobo suna cikin ‘yan kwallon Najeriya da suka kai zagaye na 16 a gasar cin kofin duniya na shekarar 2014. Yaya Toure da ‘yan kwallon kafan Ivory Coast sun kasa wuce zagayaen farko a wasan kwallon cin kofin duniya amma duk da haka sun yi wasa mai armashi.
Toure, Musa da Yobo duk ‘yan kungiyoyin kulab-kulab ne da suka ci gasar rukunoninsu a shekarar wasa ta 2013-2914, yayin da Enyeama ya taimaki Lille ta samu matsayi na uku a gasar kulab-kulab na daya na Faransa duk da tsananin fafatawa da suka yi da Paris Saint-Geraine da AS Monaco.
Enyeama dan shekara 31 da haihuwa ya yi shekara da shekaru yana kwallo a Najeriya da kasar Israila ya koma Lille a shekarar 2011 kuma Rene Girard ya daukeshi karon farko a matsayin mai tsaron gida a shekarar wasa ta 2013-2014. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya sakama Garcia da hana kwallo da yawa wucewa cikin raga a kungiyoyin rukuni na daya kuma sun yi wasa na mintuna 1,062 ba tare da wani ya jefa masa kwallo a ragar gidan da yake tsarewa ba lamarin da ya sa ya zo cikin mintuna 114 na rukunin. Ba shakka Lille zata dogara ga Enyeama shekara mai zuwa domin ta cimma muradunta na cin kofin rukuni na daya.
Ahmed Musa dan shekara 21 yana da hazaka da damar da zai iya zama zakaran ‘yan kwallon Najeriya nan gaba. Wannan matashin yana kungiyar CSKA Moscow tun shakarar 2012 kuma kwallaye 7 da ya saka a raga cikin wasanni 26 da yayi sun taimaki CSKA Moscow ta ci kofin Russian Premier League. ’Yan kallon wasan kwallon Najeriya yakamata su yi murna musamman ganin cewa Musa shi ne ya zama dan Najeriya na farko da zai saka kwallo cikin raga fiye da sau daya a wasan FIFA na cin kofin duniya bayan ya saka kwallo sau biyu a gidan ‘yan wasan Argentina wadda ita ce ta zo ta biyu a gasar cin kofin duniya na 2014.
Joseph Yob dan shekara 33 jigo ne a wajen tsaron ‘yan wasan Najeriya kuma yayi fice. Yobo ya soma wasa ne a tsakiyar shekarar wasa ta 2013-2014 a Turkiya da kungiyar da ta zama zakara ta kasar wato Fenerbahce kafin a bayar dashi aro ga Norwich City ta Ingila. Yobo ya fara wasansa da Norwich City inda ya taka rawar gani a karawarsu da kungiyar Yaya Toure ta Manchester City. Yobo ya kafa gidauniya ta jinkai da ya sawa suna Joseph Yobo Charity Foundation wadda ke taimakawa yara mara galihu a Najeriya da biyan kudin makarantarsu.
Toure dan shakara 31 kwararre a wasan kwallo ya ci gasar 2012 da 2014 ta Firimiya da ta 2009 na UEFA, sai kuma a shekararun 2011,2012 da 2013 da aka zabeshi zakaran ‘yan kwallon Afirka. Yaya Toure ya ci kofuna da dama amma yana ci gaba da kokarin a amince dashi a matsayin dan kwallon da ya fi fice na wannan shekara. Toure jakadan fatan alheri ne na shirin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya sabili da fafitikar da yayi na hana kashe giwaye
Facebook Forum